Merkel ta nemi hadin kan Akufo-Addo kan hijira
August 30, 2018Bindigar karramawa 21 sojojin Ghana suka buga a filin jirgin sama na Accra don tarbar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Wannan shi ne karon farko da ta amsa goron gayyatar da hukumomin Ghana suka yi mata, tun bayan yada zango da ta yi a Accra a kan hanyarta ta zuwa kofin duniya na kwallon kafa a 2010 a Afirka ta Kudu.
Merkel ta je Ghana ne saboda kaurin suna da ‘yan kasar suka yi wajen kwarara nahiyar Turai don neman kudi. Alkaluma sun nunar da cewar hukumomin Jamus sun yi watsi da takardun neman mafaka na ‘yan Ghana 4200. Tun bayan da Jamus ta fara fuskantar rarrabuwar kawunan dangane da tarar ‘yan gudun hijira shekaru ukun da suka gabata, shugabar gwamnati Angela Merjel ta fara hada gwiwa da wasu kasashen Afirka wajen dakile kwararsu. Sannan a daya hannun Jamus ta yi wani "garambawul na cinikayya" inda take neman bai wa Afirka wani matsayi na musamman.
Ministan raya kasa na Jamus Gerd Müller wanda shi ma ke ziyarar aiki a Accra ya yi kira ga ‘yan kasuwar kasarsa da su kara hannayen jarinsu a Ghana. Kimanin kamfanonin Jamus 80 daga guda 1,000 da ke aiki a Afirka ne ke da cibiya a Ghana. Musayar kasuwancin tsakanin Ghana da Jamus na zama kashi daya cikin goma na cinikayya da kasashe kamar Kuroshiya ko Kazastan, in ji Müller.
Shugaban kasar Nana Akufo-Addo na son zamanantar da tsarin tattalin arziki na kasarsa, tare da kawo karshen dogaro a kan taimakon raya kasa daga yammacin duniya. Ko da yake Ghana na kokarin rage bashin da ke kanta, amma kuma tattalin arziki kasar da ta kunshi mutane miliyan 29 na bunkasa.
Akufo-Addo na kokarin shawo kan dubban 'yan Ghana da su yi watsi da akidar zuwa Turai ta hanyoyin da ba su dace ba. Bisa ga alkalulan Hukumar Hijjra ta duniya, a watan Maris kusan ‘Yan Ghana 2,500 suna zaune a kasar Libiya, lamarin da ya sanya su a matsayi na biyar na ‘yan Afirka da ke neman shiga Turai ta ko halin kaka.
‘Yan Ghana ba su da harumin neman mafaka a Turai saboda Jamus ta riga ta sanya kasar ta yammacin Afirka a matsayin wacce ba a fama da rikici ko tashin hankali.