1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta nuna takaicin yakin Rasha a Ukraine

June 8, 2022

A karon farko tun bayan barin mulkin Tayarayyar Jamus, tsohuwar shugabar gwamnatin kasar, Angela Merkel ta yi jawabi game da yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine.

https://p.dw.com/p/4COiQ
Deutschland Altkanzlerin Merkel zu Gespräch im Berliner Ensemble
Hoto: Fabian Sommer/dpa/picture alliance

Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta bayyana takaicin yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine, matsalar da ta ce ta yi iya kokarinta na ganin ta kare aukuwar ta a zamanin da take aiki.

A wani taron manema labarai da ta yi a karon farko tun bayan barin ta aiki, Angela Merkel ta ce mamaya mara kan gado da Rasha ta kai wa Ukraine ya yi hannun riga da muradun martaba hakkokin bil Adama.

Yayin da take magana a kan yarjejeniyar birnin Minsk ta 2014 da aka cimma da Rasha, Merkel ta ce ko kadan ba za ta dauki laifin gazawa wajen shawo kan Rasha.

Angela Merkel wacce ta jagoranci kasashen Yamma wajen kakaba wa Rasha takunkumai a 2014 saboda kwace yankin Crimea da ta yi, ta ce matakin ne ya bai wa Ukraine damar kasancewar kasar da take a yau.