Merkel ta nuna takaicinta kan harin Berlin
December 20, 2016Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana takaicinta dangane da abin da ta kira harin ta'addancin da aka kai a wata kasuwar Kiristimeti ta birnin Berlin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12. Ta bayyana haka ne lokacin wani taron manema labarai a wannan Talata a birnin Berlin inda ta sha alwashin gudanar da kwakwaran bincike a kai dama yin hukunci mai tsanani kan wadanda ke da hannu a cikinsa inda ta yi karin bayani tana mai cewa:
"Ta ce ya zuwa yanzu akwai abubuwa da dama da ba mu sani ba da kuma ba mu da tabbaci kansu, amma dai a bisa manufa za mu iya cewa harin ta'addanci ne"
Sai dai hukumar 'yan sandar kasar ta Jamus ta sanar da kame wani matashi dan shekaru 23 dan asalin kasar Pakistan wanda ake zargi da kai harin da gangan da motar wacce ake zaton ita kanta ya kwace ta ne daga hannu wani direban dan asalin kasar Poland wanda aka iske gawarsa a cikin motar bayan afkuwar lamarin.
Sai dai ministan cikin gida na aksar ta Jamus Thomas de Maiziere ya sanar da cewa mutuman ya musanta zargin da ake yi masa, amma suna ci gaba da bincike a kai. Amma kuma wasu rahotanni na baya bayan nan na cewa wani babba daga cikin shugabannin hukumar 'yan sandar ta Jamus ya kwarmata wa jaridar DIe Welt ta Jamus da cewa ga bisa dukkan alamu ba su kai ga kame mutaman na gaske da ya kai harin ba wanda yanzu haka ya mallaki bindiga kuma yana cikin gudu.