Merkel ta samu tabbacin kafa gwamnati
January 12, 2018Talla
Shugaban jam'iyyar SPD Martin Schulz ya shaida wa manema labarai a daren Alhamis zuwa Juma'a cewar jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta amince kan a yi hadakar ne bisa sharadin wasu manufofi da za su taimaka wa kasar. An yi zaben na Jamus tun sama da watanni uku da suka gabata. Sai dai har yanzu ba a kai ga kafa gwamnati ba saboda gaza cimma matsaya daga wasu jam'iyyun da za a kafa gwamnatin hadakar tare da su.
Har yanzu shugabannin jam'iyyar SPD na ci gaba da tallan batun hadakar ga sauran 'yan jam'iyyar, kuma nan gaba za su yi babban taro a birnin Bonn don duba yiwuwar amincewa da shi ko akasin haka. Kafa gwamnati dai ita ce kadai hanyar da za ta sa a kauce wa kafa gwamnatin marasa rinjaye ko kuma a sake sabon zabe a Jamus.