1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta shawarci mahukuntan kasar Sin

Zulaiha Abubakar
May 25, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana samar da cikakken tsaron bayanai a matasayin kashin bayan dorewar kasuwanci a kasar Chaina yayin kammala ziyarar aikin da ta kai kasar.

https://p.dw.com/p/2yKa2
Angela Merkel da Xi Jinping
Angela Merkel da Xi Jinping Hoto: picture alliance/AP Photo/J. Lee

Merkel ta kuma kara da cewar a yayin ziyarar ta jaddadawa mahukuntan kasar ta Chaina muhimmancin tsare ayyukan sirri na fadar mulki ta Beijing a kafar sadarwa ,wanda ke yawan samun kutse sakamakon rashin daukar ingantattun matakan tsaro, daga nan sai ta bayyana aniyarta ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Jamus da Chaina a kan motoci marasa matuki don ayyukan tsaro.

Wannan Ziyara ta Angela Merkel na zuwa ne a daidai lokacin da fadar mulki ta kasar Chainan ke fuskantar tsamin danganta tsakanin ta da kasashen Iran da Koriya ta Arewa.