1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta soki lamirin gwamnatin Turkiya

June 17, 2013

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce dole ne hukumomin a kasar Turkiya su yarda da 'yancin fadin albarkacin baki ko da na sukar gwamnati ne.

https://p.dw.com/p/18rDu
Protesters are confronted by police during a demonstration at Kizilay square in central Ankara June 16, 2013. Thousands of people took to the streets of Istanbul overnight on Sunday, erecting barricades and starting bonfires, after riot police firing teargas and water cannon stormed a park at the centre of two weeks of anti-government unrest. Lines of police backed by armoured vehicles sealed off Taksim Square in the centre of the city as officers raided the adjoining Gezi Park late on Saturday, where protesters had been camped in a ramshackle settlement of tents. REUTERS/Dado Ruvic (TURKEY - Tags: CIVIL UNREST POLITICS)
Hoto: Reuters

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki matakin ba sani ba sabo da 'yan sandar Turkiya ke dauka a kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a birnin Santambul da sauran biranen kasar. A wata hira da aka yi da ita gabanin ta tashi zuwa taron kolin kasashen Kungiyar G-8 a yankin Ireland ta Arewa, Merkel ta ce dole ne sabuwar kasar Turkiya ta amince cewar mutane na da 'yancin bayyana ra'ayinsu. Sai dai shugabar gwamnatin ta Jamus ta kauce daga amsar tambayar ko wannan matakin karfi da hukumomin na Turkiya ke dauka, ya dace wata kasa dake neman shiga Kungiyar Tarayyar Turai EU ta dauka. Shaidu sun rawaito cewa a cikin daren Lahadi zuwa safiyar Ltinin 'yan sanda a biranen Santambul da Ankara sun yi amfani da karfi fiye da kima a kan masu boren kin jinin gwamnati. Don nuna adawa da matakan da 'yan sandar ke dauka a kan masu zanga-zangar, manyan kungiyoyin kwadago biyu a kasar sun kira da a gudanar da yajin aiki. Sai dai ministan cikin gida ya kira matakin 'yan kwadagon da cewa haramtacce ne.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas