1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yaba dangantakar kasa da kasa

Abdullahi Tanko Bala
June 18, 2021

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yaba wa kudirin shugaban Amirka Joe Biden na farfado da ruhin dangantaka tsakanin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/3vCDc
Deutschland Treffen Merkel und Macron in Berlin
Hoto: Axel Schmidt/dpa/Reuters/picture alliance

Merkel wadda ta baiyana haka a birnin Berlin a taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban Faransa Emmanuel Macron ta baiyana farin ciki da cewa shugaban Amirka ya sake samar da wani yanayin kawance da kowace kasa za ta yi abin da ya kamata.

Ta kara da cewa ya kamata kungiyar tarayyar Turai ta cigaba da tattaunawa da Rasha duk da banbance-banbance da ke tsakaninsu kan batutuwa da suka shafi tsaro da rikicin kasashen Ukraine da Siriya.

Shugabar gwamnatin Angela Merkel ta kuma ce akwai bukatar kasashen na Turai su tsara tare da tuntubar juna kan manufofinsu na annobar corona da kuma sake bude iyakoki. 

Shi ma da yake tsokaci shugaban Faransa Emmanuel Macron yace ya kamata a yi taka-tsantsan kada a sake shigo da wasu sabbin nau'in kwayar cutar zuwa cikin kasashe.