Merkel ta yi jawabi kan kuɗaɗen ceton Bankunan Turai
October 26, 2011Sao'i ƙalilan gabannin tafiyarta zuwa taron ƙungiyar tarayyar Turai EU a birnin brussels, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana a gaban majalisar dokoki ta Bundestag, domin kare manufofin gwamnatinta na ƙara yawan kuɗaɗen ceto a ƙasashen da ke amfani da kuɗin Euro. Merkel ta faɗawa 'yan majalisar ta Jamus cewar, Duniya ta sanya wa Turai da tarayyar Jamus ido domin warware wannan matsalar.
"gwamnatin tarayyar Jamus na muradin ganin cewar an daidaita matsalolin tattalin arziki. Dangane da haka ne ya zamanto wajibi, baya ga magance matsalar da muke fuskanta yanzu, mu samar da makoma ta hadin gwiwa tsakanin kasashen dake amfani da kudin Euro"
Shugabar gwamnatin ta jamus ta bayyana cewar ƙara kuɗaɗen ceton, wani mataki ne mai haɗarin gaske, sai dai ba zai dace ace an ƙi ɗaukar wannan mataki ba. Duk da rarrabuwar kawuna da ake samu tsakanin 'yan jami'yyun haɗakar mulkin kasar, ana saran cewar wannan shiri zai samu amincewa a majalisar ta Bundestag, wanda zai bawa Merkel ƙarfin mahawara kan batun.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu