Merkel ta yi marhabin da sabon wa´adin kan kundin tsarin mulkin EU
June 16, 2006Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi maraba da sabon tsarin lokacin da aka gabatar don ceto daftarin tsarin mulkin KTT. Gabanin a shiga rana ta biyu kuma ta karshe a taron kolin kungiyar EU a birnin Brussels, Merkel ta ce hakan zai bawa kundin wata sabuwar dama. A jiya mahalarta taron suka amince da karshen shekara ta 2008 ta kasance lokacin da za´a tsayar da shawara game da makomar kundin tsarin mulkin na EU. Merkel ta ce Jamus wadda zata karbi shugabancin karba-karba na kungiyar a watanni shidan farko na shekarar badi, zata ta da muhawwara akan kundin. Tun bayan da kasashe Faransa da NL suka kada kuri´ar kin tsarin mullkin a bara, aka yi watsi da shi.