1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi watsi da bukatar hade basukan turai.

June 27, 2012

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jaddada cewa babu wani yanke ko hanya mai sauki ga warware matsalolin kudade da suka addabi nahiyar turai.

https://p.dw.com/p/15Mwy
Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) spricht am Mittwoch (27.06.2012) im Bundestag in Berlin. Die Regierungschefin gab eine Regierungserklärung zum Europäischen Rat ab. Foto: Wolfgang Kumm dpa/lbn
Hoto: picture alliance/dpa

Kwana guda gabanin taron kolin shugabannin kasashen Turai da zai yanke kudiri game da makomar kasashe masu amfani da kudin euro, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi watsi da karin kiraye kiraye daga kasashen Spain da Italiya na daukar matakan gaggawa domin saukaka musu nauyin bashin dake kansu. A ranar Alhamis din nan ce shugabannin kasashen turan za su hallara a Brussels domin taron da zasu yi kwanaki biyu wanda tuni aka sami rarrabuwar kawuna irin wadda ba'a taba gani ba tun bayan da aka shiga badakalar rikicin bashin a shekarar 2010.

Da ta ke jawabi ga majalisar dokoki a birnin Berlin shugabar gwamnati Angela Merkel ta zargi manyan jami'an kungiyar tarayyar turan da yin riga malam masallaci inda suka gabatar da shawarar hade basukan kasashen na euro wuri guda tun gabanin sanya matakan lura da kasafin kudin kasashe da kuma manufofinsu na tattalin arziki.

Merkel ta ce babu wata hanya ta gaggawa ko kuma matakai masu sauki na shawo kan matsalolin, tana mai cewa mafita kawai iata ce daukar matakai sannu a hankali daya bayan daya domin ciwo kan matsalar tun daga tushe.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita Mohammad Nasiru Awal