1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta ziyarci kasuwar da aka kai hari

Gazali Abdou Tasawa
December 20, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai ziyara a wannan Talata kasuwar Kirsimeti ta birnin Berlin inda wani dan ta'adda ya halaka mutane 12 tare da jikkata wasu 48 a cikin wani hari da ya kai da babbar mota. 

https://p.dw.com/p/2UcZ3
Deutschland Angela Merkel, Thomas de Maziere und Frank-Walter Steinmeier am Breitscheidplatz
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Bayan bayyana alhininta ga mutanen da suka rasu da iyalansu Angela Merkel ta ajiye furanni a daidai wurin da aka kaddamar da harin a kasuwar. Da take jawabi a gaban manema labarai kafin ziyartar kasuwar kristiman ta birnin Berlin, Angela Merkel ta bayyana fatan ganin maharin bai kasance daga cikin jerin bakin da aka bai wa mafaka a kasar ba inda ta yi karin bayani tana mai cewa:

"Na san cewa idan dai har ta tabbata cewa mutumin da ya kai wannan hari na daga cikin mutanen da muka bai wa mafaka a kasarmu to lalle abin zai yi mana ciwo mu Jamusawa musamman wadanda a ko wace rana ke faman fadi tashin taimaka wa 'yan gudun hijira"

Angela Merkel ta kuma kara da cewa ala kulli halin wannan hari ba zai tsorata su ba, ba kuma zai sa Jamusawa su fasa gudanar da irin wadannan kasuwanni na Kristimati masu cike da tarihi ba, wadanda ke kasancewa matattarar iyalai a filin Allah ta'ala a duk karshen shekara.