G20 sun rattaba hannu kan daftarin kare muhalli
June 29, 2019Talla
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ce ta bayyana haka a yau Assabar tana mai cewa yarjejeniyar kare muhalli ta zo daidai da irin wacce kasashen suka cimma a shekarar bara, bayan shafe tsawon lokaci a na ta kai ruwa rana kafin nuna amincewar wasu kasashen game da ita.
Merkel ta ce daukacin kasashe 19 ciki har da Fransa da Jamus da China duk sun lamunta da wannan daftarin da ke kara jaddada yarjejeniyar birnin Paris kan batun dumamar yanayi baya ga Amirka kawai wacce da har yanzu ta ke ci gaba da nuna turjiya akai.