1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi wa Ukraine alkawarin goyon baya

Gazali Abdou Tasawa
November 1, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta yi wa mahukuntan kasar Ukraine samun goyon bayan kasar Jamus a yarjejeniyar zaman lafiya ta birnin Mimsk da ma ga shirin tsawaita takunkumi ga Rasha.

https://p.dw.com/p/37X84
Ukraine Besuch Angela Merkel bei Petro Poroschenko
Hoto: Reuters/Handout Ukrainian Presidential Press Service/M. Palinchak

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta yi wa mahukuntan kasar Ukraine samun goyon bayan kasar Jamus a yarjejeniyar zaman lafiya ta birnin Mimsk da ma ga shirin tsawaita takunkumin da kasashen Turai suka saka wa Rasha a sakamakon rawar da take takawa a rikicin kasar ta Ukraine. 

Merkel ta bayyana wannan matsayi nata ne a wannan Alhamis a gaban Shugaban Petro Porochenko na kasar ta Ukraine inda ta kai wata ziyarar aiki da ke zama ta farko tun bayan cimma yarjejeniyar ta Minsk a shekara ta 2015:

Ta ce "Ga zancen da muke kasashe ba sa mutunta yarjejeniyar Minsk, ci-gaban da ake samu kan batun kadan ne, dan haka Jamus za ta tashi tsaye domin ganin a watan Disemba a tsaiwaita takunkumin da aka saka wa Rasha"

 Sai dai ziyarar ta Merkel za ta kasance ta gaisu wa da rokon iri inda za ta tattauna da shugaban kasar ta Ukraine kan shirin nan da yake adawa da shi na ginan bututun jigilar gaz daga kasar ta Rusha zuwa Jamus da zai kewaye wa kasashen Ukraine da Poland da aka fi sani da sunan Nord Stream 2. Merkel za ta yi kokarin kwantar wa da mahukuntan Kiev da hankali kan  ci gaba da amfani da butun jigilar gaz da ke bi ta cikin kasar ta Ukraine ko bayan kaddamar da shirin na Nord Strem 2.