1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel za ta shugabanci CDU a karo na tara

Abdul-raheem Hassan
December 6, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi nasarar kasancewa shugabar jam'iyyar CDU a karo na tara, wannan mataki dai na zuwa ne bayan da Merkel din ta jaddada kudurinta na kare shigowar baki a kasar.

https://p.dw.com/p/2Tpze
Deutschland CDU Bundesparteitag Rede Merkel
Hoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

A wani taron fidda gwani da jam'iyyar CDU ta gudanar a wannan Talata a birnin Essen da ke yammacin Jamus, Shugabar Gwamnati Angela Merkel ta samu kaso sama da 89 cikin 100 na kuri'un wakilai. To sai dai wannan shi ne karo na farko da Merkel din ta samu karancin kuri'u tun daga shekara ta 2000. Ana danganta rashin tasirin nata sosai ne da yadda ta kafe a kan kudurinta na bude wa 'yan gudun hijira kofofin kasar.

Zamanta shugabar jam'iyyar karo na tara na zama tabbacin karawa da sauran 'yan takarar da ke zawarcin shugabancin gwamnatin Jamus a babban zaben da ke tafe a shekara mai zuwa ta 2017. Wasu na ganin cewa nasarar Merkel din ta biyo bayan daukar matakan kaffa-kaffa a kan shigowar 'yan gudun hijira, da kuma bukatar da ta yi na haramta wa mata Musulmi rufe fuska da burka a wasu wurare.