1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel:Dimukuradiyya na wanzuwa da sauyi

Abdullahi Tanko Bala
December 31, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci hadin kan 'yan kasa a jawabinta na sabuwar shekara ta 2019 don karfafa tasirin EU da hadin kai a tsakanin kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/3Ap0D
Deutschland - Neujahrsansprache Bundeskanzlerin Angela Merkel ***ACHTUNG SPERRFRIST
Hoto: picture-alliance/dpa/AFP/J. MacDougal

A jawabinta na sabuwar shekara shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga 'yan kasar su jajirce wajen daukar nauyin da Jamus za ta tukara a fagen siyasar duniya da kuma shirin sake fasalin tattalin arzikin kasar. Merkel ta ce hadin kan kasashen duniya na da matukar fa'ida wajen cimma wannan nauyi. 

"Tace fahimta ta a matsayin shugabar gwamnati dimukuradiyyarmu ta wanzu ne tare da amincewar mafi rinjayen al'umma cewa dukkan jama'a za su yi dukkan bakin iyawarsu wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya da hadin kan kasa. Za kuma su cigaba da yin waiwaye kan abin da za su iya a daidaikun su na bada gudunmawa. Wannan shine abin da na yi. Duk da yadda shekarar da ta gabata ta kasance da armashi ko akasin haka, ina ganin shekaru 13 a matsayin shugabar gwamnati sun wadatar."

A cikin jawabin Agela Merkel ta kuma yi waiwaye akan matsalolin da aka fuskanta wajen kafa gwamnati bayan zaben majalisun dokokin tarayya a 2017. Sai dai kuma shugabar gwamnati wadda 'yar jam'iyyar CDU bata yi misali kan matsalolin da aka fuskanta din ba. Ta dai sha jayayya da ministan cikin gida Horst Seehofer na CSU da ke kawance da CDU a jihar Bavaria, da kuma wata takaddamar da SPD. Dukkan rashin jituwar na da nasaba ne da batun 'yan gudun hijira.