1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Nijar ya yi murabus

Abdoulaye Mamane Amadou SBA
April 11, 2018

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa ministan harkokin wajen kasar Ibrahim Yacouba ya yi murabus daga mukaminsa, kuma jam'iyyarsa ta MPN Kishin kasa ta janye daga gun-gun jam'iyyun da ke mulki na MRN.

https://p.dw.com/p/2vtQv
Präsidentschaftskandidat Ibrahim Yacouba Niger Wahl 2016
Hoto: DW/M.Kanta

Kamar yadda wakilinmu na Yamai Abdoulaye Mamane Amadou ya ruwaito, wanda ya ce a wata ruwaya, an ce Firaministan kasar ne ya kira ministan harkokin wajen ya sanar da shi cewa shugaban kasa ya gaji da ksancewarsa minista a wannan gwamnati, inda shi kuma ya rubuta takardar murabus. Ba tun yau ba dai masana ke ta hasashen cewar danganta ta fara tsami tsakanin jam'iyyar ta MPN Kishin Kasa da abokiyar dasawarta ta PNDS Tarayya duba da wasu mahimman takardun da jam'iyyar ta ce ta aike ga wasu kusoshin gwamnati game da batun kafa hukumar zabe da ma kundin tsarin zabe dangane da shirye-shiryen zabukan kasar masu zuwa na 2021. Sai dai Jam'iyyar ta MPN ta ce duk da koke-koken da ta shigar ga gun-gun kawancen na masu mulki Jam'iyyar ta PNDS da abokan tafiyarta sun yi kememe da ma nuna mata cewar bukatar da ta shigar ba ta taka kara ta karya ba.

Haka ita ma ministar yada labarai ta kasar Hadizatou Koubra Abduollahi da ke zaman 'yar jam'iyyar ta MPN Kishin Kasa ta ajiye mukaminta. Tuni dai aka maye gurbin  Ibrahim Yacouba da Kalla Hankouraou wanda ke zaman mamba a kwamitin koli na jam'iyyar PNDS Tarayyar mai mulki, da aka taba zarga da bayar da kwangila ba bisa ka'ida ba, lokacin da yake ministan gine-gine. Ita kuwa ministar yada labaran Hadizatou Koubra Abduollahi an maye gurbinta ne da Sala Habi Mahaman Salissou, wanda a baya yake rike da mukamin ministan birane na Jamhuriyya ta Nijar.