Ministan harkokin wajen Rasha na ziyara a China
April 8, 2024A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce a yayin wannan ziyara ta kwanaki biyu Mista Lavrov zai gana da takwaransa na China Wang Yi inda za su tattauna kan wasu muhinman batutuwa da suka jibanci yakin Ukraine da kuma yankin tekun Pacifique.
Karin bayani: Sojojin China da Rasha za su yi atisaye
Bugo ta kari sanarwar ta ce jami'an diflomasiyyan guda biyu za su fi mayar da hankali kan huldar da ke tsakanin kasashensu da kuma kara karfafa hadin gwiwarsu a fagen siyasar kasa da kasa.
Karin bayani: Dangantaka tsakanin Rasha da China
Sai dai kasashen Yammacin duniya nu nuna damuwa kan kara karfin hulda tsakannin wadannan kasashen biyu, domin ko da baya-bayan nan sakatariyar baitilmanin Amurka Janet Yellen a lokacin da take ziyara a China ta yin hannuka mai sanda ga kamfanonin China da za su yi kuskuren taimaka wa Rasha kan yakin da take Ukraine.