Ministan harkokin wajen Rasha Lavrov ya sauka a Conakry
June 4, 2024Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, ya sauka a birnin Conakry na kasar Guinea a ci gaba da ziyararsa ta kasashen yammacin Afirka da ke fama da juyin mulkin sojoji, domin kara karfafa dangantaka, bayan da kasashen suka yanke alaka da Faransa da kuma Amurka.
Karin bayani:Rasha na kara zawarcin Afirka
A yayin ziyarar da ya fara ranar Litninin, Mr Lavrov ya gana da ministan harkokin wajen Guinea Morissanda Kouyate, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar. Ita kuma Guinea cewa ta yi ziyarar na da alaka da kara yaukaka dangantaka a tsakanin kasashen biyu.
Karin bayani:Rasha: Lavrov na ziyara a Afirka
Bayan kammala ziyarar Guinea Conakry, Mr Lavrov zai wuce zuwa Jamhuriyar Congo, inda zai gana da shugaba Denis Sassou N'Guesso, kamar yadda hukumomin Brazaville suka sanar.
Kasashen da Rasha ta kulla kyakkyawar alaka da su sun hada da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso, wadanda yanzu haka ke hannun sojoji bayan juyin mulki.