Kasar Girka ta yi barazana ga EU
June 30, 2015Ministan harkokin kudin kasar Girka Yanis Varoufakis ya yi barazanar daukar mataki na shari'a kan shugabannin kungiyar Tarayyar Turai idan har aka yi waje road da kasar cikin kasashe da ke amfani da kudin bai daya na Euro koda kuwa cewa mahukuntan na birnin Athens sun gaza biyan kudaden bashin da ake binsu da wa'adin ranakun biyansa ke cika a ranar Talatan nan.
Ya ce a yarjejeniyar kungiyar ta EU babu inda aka tsara cewa za a fita daga tsarin amfani da kudin na bai daya dan haka ba za su lamunta ba.
Varoufakis ya bayyana haka ne a zantawa da gidan jaridar Daily Telegraph ta Birataniya a yammacin ranar Litinin.
Firaminista Alexis Tsipras na kasar ta Girka a ranar Litinin din ya bayyana cewa kasar ta Girka ba za ta biya sama da miliyan dubu na Euro ba ga asusun bada lamuni na IMF a ranar Talatan nan har sai ta cimma matsaya da wadanda su ke binta bashi.
Dubun dubatar al'ummar kasar ta Girka dai sun fito wata zanga-zangar nuna goyon baya ga mahukuntan kasar da ke kaucewa kara aza musu sabbin matakai na tsuke bakin aljihu daga kasashen na Turai.