1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin harkokin waje na Turai na taro akan Iran

December 1, 2011

Britaniya ta nemi kara kakabawa Iran takunkumin tattalin arziki dangane da shirinta na Nukiliya

https://p.dw.com/p/13Kbr
Alain Jupe na Faransa da William Hague na BritaniyaHoto: dapd

 Britaniya ta yi kira ga ministocin harkokin waje na ƙungiyar Tarayyar Turai da su ƙara ƙaimi wajen sanya wa Iran Takunkumin tattalin arziki dangane da shirinta na Nukiliya.To sai dai har yanzu babu tabbaci ko sabbin takunkumin na turai zai shafi ɓangaren mai. Britaniya, wadda matasa suka afkawa ofishin jakadancinta dake birnin Tehran a ranar talata, ita ce  zata jagoranci gabatar da kudurin, bayan rahotan hukumar kula da makamashi, da ya nunar da cewar Iran ɗin na sarrafa boma boman Atom. Ministan harkokin wajen Britaniya Willian Hague, yayi fatan cewar takwarorin nasa na turai zasu amince da sake ɗora wa Tehran karin takunkumin tattalin arziki, da zasu tilasta mata dakatar da shirinta na Nukiliya. Tun a jiya laraba ce dai, Britaniya ta rufe ofishin jakadancin Iran da ke birnin London tare da koran dukkan ma'aikatan ofishin daga ƙasar. Sai Ministan harkokin wajen Britaniyan ya hakikance cewar, babu alakar taron ministocin harkokin wajen na yau a Brussels, da harin da aka kai wa ofishin jakadancin Britaniyan a birnin Tehran. Ana saran ministiocin Turan zasu dauki matsayi dangane da rahotan hukumar kula da makamshi ta Majalisar Ɗunkin Duniya ta gabatar akan Iran.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita           : Umaru Aliyu