1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa za su yi wani taron gaggawa kan rikicin Gabas Ta Tsakiya.

July 13, 2006
https://p.dw.com/p/Buqf

Ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa, za su yi wani taro na musamman a birnin Al-Ƙahira a ran asabar mai zuwa, don tattauna tsanantan rikicin yankin Gabas Ta Tskaiya, tsakanin Isra’ila da Lebanon da kuma Falasɗinawa. A cikin wata sanarwar da ta buga yau a birnin Al-Ƙahiran, Ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta ce, taron zai yi nazari ne kan mummunan halin da ake ciki yanzu a ƙasar Lebanon da yankin Falasɗinawa, da kuma hare-hare da barazanar da Isra’ilan ke yi musu.

A hare-haren da Isra’ilan ta yi ta kaiwa a zirin Gaza dai, a ƙalla Falasɗinawa 75 ne suka rasa rayukansu a cikin mako ɗaya.