Ministocin tsaron Rasha da Amirka sun tattauna
October 21, 2022Ganawar ta zo ne bayan ambato wasu jami'ai masu jibi da fadar mulkin Rasha ta Kremlin da aka yi suna cewa za su maida birnin Kherson da ke kudancin Ukraine a matsayin wata tunga ta dakarun Rasha.
Babu dai cikakkun bayanai kan abubuwan da manyan jami'an kasashen biyu, da Sergei Shoigu na Rasha da kuma Lloyd Austin na Amirka suka tattauna a kansa.
Sai dai abin da ya bayyana shi ne batutuwan tsaron kasa-da-kasa na daga ciki, da ma batun da ya danganci yakin Ukraine.
Sakataren tsaron Amirka Lloyd Austin, ya jaddada bukatar dorewar sadarwa a tsakaninsu, inda ya yi kiran Rasha da ta kaddamar da shirin tsagaita bude wuta a Ukraine.
Wannan ya zo ne yayin da aka fatattaki dakarun Rasha daga Kyiv babban birnin kasar Ukraine, amma kuwa suke samun galaba a yankunan Dombas da Kharkiv daga kudanci.