1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar ministocin Turai da na Iran

Yusuf Bala Nayaya
May 11, 2018

Wannan tattaunawa dai na zuwa ne bayan da Amirka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran wacce kasashen na Jamus da Faransa da Birtaniya da Rasha da China suka sanya hannu.

https://p.dw.com/p/2xXWM
Luxemburg EU-Außenministertreffen
Tattaunawar ministocin harkokin wajen kasashen Jamus da Faransa da BirtaniyaHoto: Getty Images/AFP/E. Dunand

Ministocin harkokin kasashen waje na Jamus da Faransa da Birtaniya za su gana da takwaransu na kasar Iran Mohammad Javad Zarif a birnin Brussels na Beljiyam tare da shugabar sashin kula da harkokin kasashen waje na Kungiyar EU a ranar Talata kamar yadda  ofishin na Federica Mogherini ya bayyana.

Mogherini za ta fara tattaunawa da ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas da na Faransa Jean-Yves Le Drian da ministan harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson kafin gaba daya su gana da Zarif na Iran.

Wannan tattaunawa dai na zuwa bayan da Amirka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran wacce kasashen na Jamus da Faransa da Birtaniya da Rasha da China suka sanya hannu.