Nijar: Mahamane Ousmane na kara samun karbuwa
February 18, 2021A daidai lokacin da aski ke ci gaba da kawowa gaban goshi a game da kammala yakin neman zabe zagaye na biyu, wasu magoya bayan jam’iyyar MNSD Nasara rashen jihar Maradi, sun fitar da sanarwar marawa dan takara Alhaji Mahamane Ousmane baya, a sabanin matakin da shugabanin hukumar koli na jam'iyyar da suka kulla kawance na goyon bayan dan takarar PNDS Bazoum Mohamed. Aski ya zo gaban goshi
Sabuwa dai ba ta karewa a fagen siyasar jamhuriyar Nijar, don kuwa a wurin taron gangamin yakin neman zabe na dan takarar Canji da ya jagoranta a birnin Maradi, shugaban jam’iyyar MNSD reshen jihar Maradi, Malam Janaidu Gado Sabo, ya baiyana sanarwa kawo goyon bayansu ga dan takara Alhaji Mahamane Ousmane, duk da ya ke uwar jam'iyyar ta kulla kawance na kawo goyon baya ga dan takarar PNDS Bazoum Mohamed. Wacce alkibla siyasar kasar ta dosa?
Tuni dai bangaren Alhaji Sain Umaru suka maida martanin rashin jin dadinsu a kan wannan mataki. Sanin kowane tun farko, reshen jam’iyyar na jiha bai goyi bayan matakin uwar jamiyyar ba, saboda haka jadaddawa ne suka yi kuma da amincewar galibinsu kamar yadda Haladu Garba wanda aka fi sani da Mai Gari shugaban jam’iyyar na reshen unguwar Burja birnin Maradi. Yanzu dai, an kamo hanyar sa kafar wando guda tsakanin uwar gijiyar jam'iyyar da rashenta na jihar Maradi, abun jira a gani dai, shi ne tasirin ko akasin haka da wannan goyan bayan zai yi a ranar 21 Febrairu mai zuwa, da ake gudanar da babban zaben zagaye na biyu.