1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman izini kan allurar Covid 19

Zainab Mohammed Abubakar
November 30, 2020

Kamfanin na neman 'yancin aiki da allurar ne, bayan mataki na uku na gwaji kan mutane dubu 30 da ke nuni da kariyar kaso 94 daga cikin 100 daga kamuwa da COVID 19.

https://p.dw.com/p/3m1Ay
Coronavirus Impfstoff Symbolbid
Hoto: picture alliance/dpa

Kamfanin sarrafa magunguna na Moderna da ke Amurka, ya sanar da kammala shirin neman izinin amfani da allurar riga kafin corona daga hukumar tantance ingancin magunguna da abincin Amurkar da takwararta ta Turai.

Kamfanin na zai gabatar da dukkan takardun neman amincewar hukumomin biyu, domin ya samu damar yin allurar ga masu bukata cikin gaggawa, bayan tabbatar da sahihancinsa.

Gwajin da aka yi wa mutane dubu 30 a cewar kamfanin, bai nuna wata alamar barazana ga lafiyar mutane ba.