Dambarwar rikicin siyasa a Iraki
August 30, 2022Talla
Babban malamin shi'a na Iraki Moqtada al-Sadr ya fara yajin aikin cin abinci har sai jami'an tsaron kasar sun dakatar da abin da ya kira ''cin zarafi da amfani da makami a kan magoya bayansa''.
Tashin hankali dai ya biyo bayan furucin al-Sadr na janyewa daga harkokin siyasa a kasar da ke cikin rikicin shugabanci da kawo yanzu ba a tsayar da takamaiman shugaban kasa da firaminista ba.
Jim kadan bayan kalaman malamin, mabiyansa suka kutsa kai cikin gine-ginen gwamnati a yankin da ake yi wa lakabi da ''green zone'' mai matukar tsaro, inda suka fara artabu da jami'an tsaro.