Kasar Morocco ta yanke harkar jakadanci da Iran
May 2, 2018Talla
Ministan harkokin kasashen wajen Morocco Nasser Bourita ya shaidawa manema labarai cewar, ya sanarwa da takwaransa na Iran cewar babu sauran huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu, bayan da ya gabatar masa da gamsassun shaidu a kan zargin, lamarin da ya sanya jakadan Moroccon barin birnin Tehran jim kadan bayan gwamnatin kasar ta umarci Iran akan tayi gaggawar rufe ofishin jakadancinta na Morocco,duk kuwa da cewar har yanzu Iran bata musanta wannan zargi ba.
A nata bangaren kungiyar Hezbollah ta rabawa manema labarai wata sanarwa mai dauke da cewar, zargin bashi da tushe tare kuma da ayyana Moroccon a matsayin 'yar amshin shatan kasashen Amirka da Isra'ila da kuma Saudi Arebiya.