1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moroko ta tsare daya cikin maharan Paris

Yusuf BalaJanuary 19, 2016

Kasar ta bayyana cewa mutumin da aka kama shi a ranar Juma'a a birnin Al-Muhammadiya na alaka ta kai tsaye da wasu maharan.

https://p.dw.com/p/1HfjW
Marokko, Anti-Terroreinheit
Jami'in yaki da ta'addanci a MorokoHoto: picture alliance/AP Images/A. Bounhar

Mahukunta a kasar Moroko sun bayyana cafke wani mutum dan kasar Belgium da ke da tsatso na kasar Moroko saboda alakarsa ta kai tsaye da wadanda suka kitsa kai hari a watan Nuwamba a birnin Paris.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Moroko ta bayyana cewa mutumin da aka kama shi a ranar Juma'a a birnin Al-Muhammadiya wanda ke zama kusa da gabar teku kusa da Casabalanca da Rabat nada alaka ta kai tsaye da wasu cikin wadanda suka kai harin na birnin Paris.

A jawabin da ma'aikatar ta fitar ta bayyana cewa mutumin ya yi tafiya zuwa Siriya tare da daya daga cikiin wadanda suka tashi bam da ke jikinsu a Arewacin birnin Paris a lardin Saint Denis kusa da filin wasa na kasa. Mutumin da ba a bayyana sunansa ba lokacin yana Siriya ya shiga kungiya ta Al'ka'ida reshen Al-Nusrakafin daga bisani ya kulla alaka da kungiyar IS wacce ke ikirarin kai harin na birnin Paris.