Mosul: Karuwar matsalar karancin ruwan sha
December 1, 2016Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai kananan yara da mata masu juna biyu da matsalar rashin ruwan sha ta fi shafa. Lugujen wuta da dakarun kawancen Iraki ke kaiwa mayakan IS ya haddasa karancin da sauran kayan more rayuwa ga mazauna birnin Mosul.
Jami'ar tsare-tsaren ayyukan jin kan bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya a Iraki, Lise Grande ta ce akwai bukatar kai agajin gaggawa ga dubban fararen hula da ke cikin matsin rayuwa.
A tun watan da ya gabata ne dai dakarun hadin guiwa suka kaddamar da yakin taron dangi da nufin mai da birnin Mosul karkashin ikon gwamnati da kungiyar IS ke iko da shi sama da shekaru biyu baya.