1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Motoci 280 na kayan agaji sun shiga Gaza

Abdullahi Tanko Bala
January 21, 2025

Manyan motoci kimanin 280 dauke da kayan agaji daga Masar sun shiga zirin Gaza a rana ta uku ta yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Israila da Hamas.

https://p.dw.com/p/4pROk
Motocin kayan agaji a iyakar Rafah da Gaza
Motocin kayan agaji a iyakar Rafah da GazaHoto: Mohamed Abd El Ghany/REUTERS

Motocin sun shiga Gaza ne ta mashigin Rafah da ke kan iyaka da Masar inda daga nan aka yi musu jagora ta mashigin Kerem Shalom  ta tsallaken iyakar Isra'ila domin hukumomin su bincika tare da bayar da sahalewar su wuce zuwa Gaza.

Daga cikin motocin da suka shiga Gaza sun hada da tankokin mai 25 kamar yadda wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa.

Tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki a ranar lahadi manyan motocin kayan agaji fiye da 1,700 suka tsallaka daga Masar zuwa zirin Gaza a cewar wakilai. Akwai kuma karin motoci kimanin 4000 da suke jiran shiga yankin na Gaza.