Jam'aa na ficewa daga Cabo Delgado saboda 'yan ta'adda
February 27, 2024Talla
Sama da mutane dubu 67suka rasa matsugunansu in ji mai magana da yawun gwamnati Filimao Suaze a wani taron manema labarai da ya yi a birnin Maputo,yayin da yake magana kan halin da ake ciki a lardin Cabo Delgado. Kusan mutane dubu biyar ne aka kashe yayin da wasu miliyan guda suka rasa muhallansu tun farkon rikicin a yankin na Cabo Delgado inda masu jihadi ke kai hare-hare.