1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsawaita wa#adin dakarun soji a Mozambik

Zainab Mohammed Abubakar
October 5, 2021

Shugabannin kasashen yankin kudancin Afirka sun amince da tsawaita wa'adin aikin rundunar sojin kwantar da tarzomar mayakan jihadi da suka addabi yankin arewacin Mozambik.

https://p.dw.com/p/41J9n
Feierlichkeiten zum Tag der Streitkräfte in Mosambik
Hoto: Estácio Valoi/DW

A bangaren yarjejeniyar da membobin kasashen 16 na kungiyar raya kudancin Afirka ta SADC suka cimma a watan Yuni ne dai, aka tura ayarin dakarun hadakar zuwa Mozambik din a watan Yuli don aikin watanni uku.

Sanarwar offishin shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa da ke rike da shugabancin SADC ta ce, shugabannin Botswana da Namibiya da Mozambik da ke taro a birnin Pretoria sun amince cewar rundunar yaki da ayyukan ta'addanci da tarzomar da gundumar Cabo Delgado ke fuskanta, da wa'adin ta ke karewa a ranar 15 ga watan Oktoba, za ta cigaba da aiki.

Rikicin arewacin Mozambik din da ya kara ta'azzara a shekarar da ta gabata dai, ya yi sanadiyyar rayukan mutane 3,340, daura da korar mutane dubu 800 daga matsugunnensu.