1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhalli: Kungiyoyin Neja Delta za su dauki makamai

Muhammad Bello M. Ahiwa
July 27, 2023

'Yan kabilar Ijaw na yankin Neja Delta a Najeriya da wasu ‘yan bindiga, sun yi barazanar fara afka wa wuraren da ake hakar mai, in har ba a hana kamfanoni fitar da hayaki mai guba ba.

https://p.dw.com/p/4UUJQ
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Bayan sauya shugabancin majalisar kabilar ta Ijaw a yankin ne a jiya, kungiyar ta ce ba za ta lamunci kamfanonin ayyukan hako mai su ci gaba da kona gas mai tattare da bakin hayaki mai guba ba, wadda kuma ke gauraye sassan garuruwan alummomi ba a yankin.

Haka kuma wata kungiyar ‘yan bindiga a yankin mai suna Creek Reform Warriors, ita kuma barazanar sa kafar wando daya ta yi da kamfanin mai na Shell, inda kungiyar ta yi zargin kamfanin ba ya martaba yarjeniyoyi da a ka rattaba wa hannu tsakanin kamfanin da kuma al‘umomin da ke makwabtar inda yake aikin hako mai.

Tuni dai kungiyar ta Ijaw ta nunar cewar za ta sake sabuwar fafutukar nema wa yankin na Neja Delta ‘yancin sarrafa ma‘adinan danyen mai da gas din yankin a hannayen ‘yan Neja Delta, tare da jaddada cewar an yi ta yi musu romon baka kan arzikin yankin nasu.

Gwamnatin Najeriya dai gami da kamfanonin na mai da ke aikin lalubowa tare da hako mai, sun yi ta cimma gabar daina kona iskar ta gas sau tari, to sai dai ba su iya cika maganar tasu ba, al‘amarin kuma da ‘yan yankin ke kukan yadda yanayin ke haifar musu da nakasu ga rayuwarsu da ma muhallinsu.

Najeriyar dai kan samu kaso kusan 80 cikin 100 na kudaden shigarta ne daga cinikin na danyen mai.

Kasar ta samu kimanin ala biliyan 46 daga cinikin na mai a shekarar 2022 kadai, bisa alkaluman hukumar tattara kididdiga ta kasa NBS.

Sai dai gazawar kasar na iya fidda gangunan danyan mai da OPEC ta sahale mata na miliyan daya da dubu 800 na dada bayyana, musamman a watan Mayu da ya gabata.

Shekara da shekaru dai, an nunar Najeriya ta dara ko wace kasa mai arzikin mai a nahiyar Afrika, hakar mai sai dai kawai, rashin tsari da kuma katutun cin hanci da rashawa, suka hana y‘an kasar su san ana yi.