Muhawara a Jamus kan matakan tsaro
December 20, 2012Yayin da yan sanda suke matsa lambar tabbatar da karin na'urorin, masu da'awar kare hakkin jama'a suna nuna cewar yin haka zai sabawa matakan kare yanci da sirrin jama'a a kasar ta Jamus.
A birnin na Bonn, an yi kokarin sanya bom a babbar tashar jiragen kasa dake tsakiyar garin, inda ko da shike akwai na'urori na daukar hotunan video bisa manufar kare lafiya da tsaron jama'a, amma yan sanda sun yi korafin cewar a daidai lokacin da aka ajiye jakar dake dauke da bom din, wadannan na'urori sun kasa daukar hotunan wanda yayi kokarin harin. Cem Özdemir, shugaban jam'iyar Greens ta masu rajin kare muhalli yace komai yawan na'urorin daukar hotunan da za'a sanya, idan basa aiki, sun zama basu da wnai amfani. Ko da shike kamfanin jiragen kasa na Jamus yana da irin wadannan na'urori a tashar, amma sai a wani wuri dabam ne wata na'urar ta dauki hoton mutumin da ake zaton shine yayi kokarin kaiwa tashar harin bom. Yan sanda da masu bincike sun baiyana zaton cewar musulmi yan darikar Salafiya ne suka yi kokarin aiwakata wnanan mummunan abu, saboda haka ministan cikin gida na taraiya, Hans-Peter Friedrich yace ana bkatar fadada matakan tsaro a manyan wuraren taruwar jama'a ta hanyar kara yawan na'urorin daukar hotunan video. To sai dai Frank Neubacher masani a fannin manyan laifuka a jami'ar Cologne yace:
"Sanya na'urorin daukar hotunan Video a manyan wuraren taruwar jama'a ba zai hana aikata manyan laifuka ga duk wadanda suka so yin haka ba, ko kuma gano wadanda suka aikata mkanyan laifukan idan suka faru. Ayi tunanin wurare masu yawa da tuni aka kakkafa masu na'urorin daukar hotunan, kamar a ababen tafiye-tafiye, amma hakan bai kawo hana aikata manyan laifuka ba."
Kamar dai a Bonn, kantuna da wuraren ciniki na yan kasuwa masu zaman kansu suna da matakan da suka dauka na tsaro, ta amfani da na'urorin daukar hotunan na video, wadanda idan hali ya samu, yan sanda suke iya amfani da hotunan da aka dauka. To sai dai wnanan hadin kai, na ganin dama ne. Duk da haka, Reinhold Bergmann, kakakin hukumar yan sanda ta Munich yace yan sandan suna bukatar karin na'urori na kansu, yadda ba sai sun dogara ga masu kantuna ko yan kasuwa ba. Idan akwai irin wadannan na'urori, yan sandan suna iya nazari da binciken hhotunan da suka dauka da zaran bukatar hakan ta taso, kamar yadda aka gani, lokacin da wasu yan tarzoma suka so tayar da boma-bamai a tashar jiragen kasa ta Cologne. Bergmann yace wannan hadari na Cologne ya nuna cewar yan sandan sun kasance a halin da suka iya samun hotunan mutanen da ake zarinsu da kokarin kai harin da nazarin yadda suka yi wannan kokari, abin da inda babu wadannan na'urori da hakan bai samu ba.
Shugaban jam'iyar Greens Cem Özdemir dake adawa da kara na'urorin daukar hotunan na Video a wuraren taruwar jama'a, yace jkamata yai a maida hankali a wnai fannin dabam domin rigakafi. Ana sane da cewar birnin Bonn, dandali ne na musulmi masu bin darikar Salafiya, ko da shike gaba daya wannan rukuni na musulmi yan kalilan ne a Jamus.
"Yace mafi yawan musulmi suna kyama, suna kuma tir da darikar Salafiya, saboda suna daukar wnanan darika a matsayin barazana ga tsarin rayuwar addinin musulunci. Musulmin basu da wata dangantaka kuma suna yaki da wnanan darika. saboda haka Salafiya bgata da wata hanya ta kara karfi a Jamus. Abin da musulmi a kasar suke bukata shine goyon baya a yakin nasu kan darikar, wanda kuma basa samun hakan."
Dan siyasar yace a ganinsa ma, karin yan sanda a kan tituna zai fi tabbatar da tsaron jama'a, fiye da kara yawan na'urorin daukar hotunan Video a wuraren taruwarsu.