Muhawara kan bincikar gwamnatin Jonathan
May 28, 2015Masu wannan bukata suka ce ya na da muhimmanci gwamnatin Buhari ta yi bincike kan yadda aka tafiyar da kasar a iya shekarun da Jonathan ya shafe ya na mulki duba da irin abinda suka ce an tafka wanda suka kai ga jefa talaka cikin mawuyacin hali. Daga cikin wuraren da suke so a tsananta bincike har da kamfanin samar da mai na kasar na NNPC da ake ganin ma'aikatansa da ministan man fetur sun yi wadaka da dukiyar kasa.
To sai dai Shugaba Jonathan din na ganin bai kamata a ce shi kadai za a bincika ba, inda ya ke cewar in har gwamnatin Buhari za ta bincike shi to ya kyautu ta binciki gwamnatocin da suka gabace shi. Wannan zuwa ne bayan da a ranar Alhamis (28.05.2015) Jonathan din ya mikawa sabuwar gwamnati bayanan mulkin kasar a wani bikin da aka gudanar a cikin fadar shugaban kasar.
Bayanan dai sun kunshi irin dabarun mulkin kasar dama irin aiyyukan da gwamnatin ta Jonthan ta yi nasarar samu a shekarun mulkinta. Senata Bala Mohammed dai na zaman daya a cikin ministocin gwamnatin Jonathan da suka halarci bikin, inda ya ke cewar kunshin bayanan da gwamnatinsu ta bada za su taimakwa gwamnatin Muhammadu buhari wajen gudanar da mulki.
Sabuwar gwamnatin Najeriya din dai na da dumbin kalubale da za ta fuskanta kama daga cin hanci da rashawa da rashin wutar lantarki da rashin aikin yi musamman ga matasa gami da tabarbarewar Ilimi da kiwon lafiya. Al'ummar Najeriya dai na zuba idanu don ganin kamun ludayn sabuwar gwamnatin wanda da dama ke fatan za ta kawo sauyi a kasar.