Muhawarar 'yan takarar shugabancin Jamus
September 13, 2021Muhawarar da gidan talabijin ARD/ZDF suka gudanar an kwashe tsawon awa guda da rabi ana tattaunawa a tsakanin dan takarar jam'iyyar CDU ta 'yan mazan jiya Armin Laschet da na jam'iyyar SPD ma su sassaucin ra'ayi da kuma ta jam'iyyar The Greens masu ra'ayin kare Muhalli Annelena Baerbock.
Wannan muhawarar ita ce ta biyu daga cikin uku da 'yan takarar za su gudanar kafin zaben da ke tafe a ranar 26 na wannan wata na Satumba da muke ciki, domin maye gurbin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wacce ta kwashe tawon shekaru 16 tana jan ragamar mulkin Jamus.
Muhawarar ta tabo bangarori da dama kama daga batun binciken kudaden haram da aka yi wa dan takarar SPD Olaf Scholz da ke zama ministan kudi, da batun rashin jituwa da dan takarar CDU ke yi da wasu 'yan jam'iyyarsa, nuna wa juna yatsa da 'yan takarar biyu suka fara da shi ya bai wa 'yar takarar jam'iyyar The Greens Annalena baerbock damar baza hajarta inda ta ce, tabbas wadannan mutanen biyu na da matsalar da Jamusawa ya kamata su kauce ma zaben su.''Ya ce zan dage kai da fata wajen ganin an maido da mutunta al'umma, za mu tabbatar da kowa ne cigaba na al'umma, za mu martaba shi ba kawai a lokacin wannan annoba ta corona ba har ma bayanta, za mu tabbatar da masu daukar karamin albashi sun sami biya mai tsoka kuma a lokacin da suka yi ritaya, su sami abin da zai rike su, duk wadannan za su yiwu idan kuka zabi jam'iyyar mu ta SPD"
A na shi bangaren dan jam'iyyar CDU kuma dan takarar shugabar gwamnati Angela Merkel Armin Laschet wanda tuni masu sharhi a al'amuran siyasa ke hangen jam'iyyarsa ta koma ta hammaya daga shugabancin da ta kwashe shekaru tana yi, ya baiyanan na shi tanadin da ya yi wa kasar idan har wannan hasashen da ake musu bai kai ga ci ba.
"Ya ce, ina son na zama shugaba da kowa zai yarda da shi, za ku iya aminta da ni domin kawo karshen wasu ka'idoji da muka gada kaka da kakani, zan barku ku yi abin da kuke da muradin yi bazan fada muku yadda za ku gudanar da rayuwarku ba, ko ma yadda za ku yi magana"
Da ma dai ita Annalena bearbock da ke zama kallabi a tsakanin rawuna ta jam'iyyar kare muhalli, ba ta aminta da manufofin abokanan karawar tata ba, wanda tun a farkon wannan tattaunawar da suka fara nuna wa juna 'yatsa a kan zarge-zargen da suke wa juna ta nuna cewar ita ce ta fi cancanta da a zaba.
"Mun manta da manufar mu a kan sauyin yanayi, saboda dukkaninku kun nuna ba ku da wani tanadi da ke da nufin fitar damu daga wannan halin da muke ciki, sai ma yadda kuke nuna wa junanku yatsa a kan wane ya toshe kaza wane ya kare kaza, idan har za mu tattauna a kan mai gobe za ta haifar, a kan wannan zaben da samar da sabuwar gwamnati da za ta tsaya kai da fata wajen ganin ta dage a kan batun sauyin yanayi wanda ke nufin kawar da makamashin kwal kafin shekarar 2038"
Abin jira a gani shi ne yadda tataunawar karshe za ta kaya tsakanin wadannan 'yan takara da ke neman shugabancin kasar ta Jamus.