Somaliya: Bama-bamai sun tashi a birnin Mogadishu
July 7, 2018Talla
Harin kuma ya jikkata wasu da dama kaman yadda babban Komandan 'yan sandan birnin Ibrahim Mohamed ya sanar, inda ta ce maharan sun yi nufin kai harin ne ga ofishin ministan cikin gidan kasar da ke kusa da majalisar dokoki. Wani jami'in agajin gaggawa mai suna Mohamed Adam, ya yi tsokaci kan abubuwan da ya gani da idanunsa:
"Kawo yanzu dai mun samu tattara wadanda suka jikkara mutun 13 a wurin da aka kai harin, kuma mun kai su a Asibiti ta Mogadiscio yanzu kuma jami'an tsaro na ci gaba da yi wa wurin kawanya."
Bayan tashin bama-baman maharan kuma sun buda wuta, kuma tuni kungiyar Al-Shabab mai alaka da kungiyar Al-Qaida a kasar ta Somaliya ta dauki alhakin kai wannan hari.