SiyasaJamus
Mummunar ambaliyar ta tilasta kwashe dubban mutane a Rasha
April 6, 2024Talla
Mahukuntan yankin da iftila'in ya shafa sun tabbatar da kubutar da matane 4,208 daga cikinsu 1,019 kananan yara ne.
Sanarwar ta kara da cewar sama da gidaje 2,500 ne mamakon ruwan saman da ya janyo fashewar dam din ya shafa.
Ma'aikatan kwana-kwanan na ci gaba da neman wasu mutamne da ake tunanin ambaliyar ta yi gaba da su.
Binciken da aka fara a kan wannan ibtila'in, an gano harda nuna halin ko in kula da ma rashin gyara wata gada da aka gina a shekarar 2014.
Shugaban kasar Khazakhstan Kassym Jomart wanda ambaliyar ya shafi wani yanki na kasar sa ya ce wannan iftila'in shi ne mafi muni da kasar ta fuskanta a sama da shekaru 80.