Mun gaji dibin bashi - Abba Gida-Gida
May 29, 2023Talla
A jawabinsa bayan shan rantsuwar kama aiki, sabon gwamnan na Kano da aka fi sani da Abba Gida-Gida ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin kusan Naira biliyan 240 da gwamnatin Dr. Ganduje ta ciyo.
Abba ya ce za su gudanar da bincike kan wadannan kudade don sanin abin da aka yi da su. Wannan batu ya haifar da mayar da maratani iri-iri daga al'ummar ta Kano sai dai ya zuwa yanzu ba wani abu daga ji daga bangaren tsohon gwamnan na Kano.
Dr. Ganduje dai ya shafe shekaru 8 yana jan ragamar gwamnatin Kano karkashin tutar jam'iyyar APC kafin daga bisani APC din ta rasa mulki biyo bayan lashe zaben da Abba Gida-Gida na jam'iyyar NNPP ya yi a 'yan watannin da suka gabata.