"Muna son zuwa Jamus"
Bayan da Hangari ta hanasu ci gaba da tafiya, dubban 'yan gudun hijira daga yankunan da ake yaki, ranar Asabar sun iso kasar da suke da burin zuwa wato Jamus. Tashar jirgin kasa ta Munich ta zama dandalin fata garesu.
Babu abin yi sai godiya
Lokacin da ya isa babbar tashar jirgin kasa ta Munich wani matashi dan gudun hijira ya nuna alamar godiya. To sai dai ba a san wanda yake wa godiyar ba. Bayan makwanni ko watanni a kan hanya, 'yan gudun hijira masu yawa sukan dauki Jamus a matsayin kasar da idan suka shigo ta sun sami tsira na hakika.
Tafiya mabudin ilimi
Wadannan 'yan gudun hijira sun kamo hanya ne tun daga Afghanistan da Iraki ko daga Siriya domin neman tsira daga yaki ko kuma aiyukan tarzoma. Suna mafarkin ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali da tsaro. Hakan yana nufin tilas kenan su kafa tushen sabuwar rayuwa. Ranar Asabar kadai, an yi kiyasin kimanin mutane 8000 ne, maza da mata da yara kanana suka isa babban birnin jihar Bavariya.
Babu wasu kaya na kirki
Mafi yawan 'yan gudun hijirar ba su samu isasshen lokaci na shirye-shiryen tafiyar tasu ba. Mafi yawansu cikin gaggawa suka tsere daga kasashen nasu, abin da ya sa kayan da suka dauko ba su da yawa.
Zaman lafiya, Kwanciyar Hankali, Salama
Ko da wane irin yare ko harshe aka fada sakon dai duk iri daya ne. Kamar sauran al'umma, su ma 'yan gudun hijirar abin da suke bukata kawai shi ne rayuwa cikin kwanciyar hankali.
Masu taimako na gaggawa
'Yan gudun hijira da yawa sun yi tafiya mai wahala cikin dare. Daga Hangari sun yi tafiya da kafa zuwa iyakar Ostiriya, kafin su sami damar shiga motoci da jiragen kasa. A babbar tashar jirgin kasa ta Munich masu agajin gaggawa na sa-kai sun yi masu marhabin da abinci da ruwan sha.
Karamin asibiti a tashar jirgin kasa
Jim kadan bayan da 'yan gudun hijirar suka isa tashar jirgin kasa ta birnin Munich an bincika lafiyarsu, saboda a kan hanyarsu ta neman tsira ba su sami magunguna ko wata hanya ta kula da lafiyarsu ko isasshen lokacin magance cututtukansu a asibitoci ba. Wasu ma daga cikinsu sun sami raunuka sakamakon yaki a kasashensu, wadanda sai a yanzu ne likitoci za su kula da su.