1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murar tsuntsaye a kasar Ukraine

December 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvID
Gwamnatin Ukraine ta kafa dokar ta-baci tare da hana fita da shiga cikin yankin tsibirin Krim inda aka samu bullar masassarar tsuntsaye. Hukumomin asibitin dabbobi sun ce an ba da umarnin kashe kaji da sauran tsuntsaye a yankin don hana yaduwar kwayoyin cutar a yankin baki daya. Sannan ma´aikatan kiwon lafiya na gudanar da bincike akan dukkan mutanen da ke da alaka da kiwon kaji ko tsuntsaye a yankin. Da farko dai an gano nau´in kwayoyin cutar ta H-5 a jikin wasu matattun tsuntsaye sama da dubu daya da 500. Yanzu haka dai ana gudanar da karin bincike a dakunan binciken kimiyya dake Birtaniya da kuma Italiya. A kuma halin da ake Indonesia ta ba da labarin mutuwar wani dan shekaru 25, wanda ya kasance mutum na 8 da masassarar tsuntsaye ta yi ajalinsa a cikin kasar.