Musayar fursunonin Rasha da Ukraine
July 17, 2024Bayan shekaru ana yaki tsakanin kasashe makobta, Rasha da Ukraine ko wace ta saki fursunonin yaki akalla 95. A cewar ma'aikatar tsaron Rasha, sojojin Rasha da ke a UKraine 95 sun iso kasar kuma dukkansu za a yi musu binciken lafiyarsu a birnin Moscow, ma'aikatar ta kara da cewa sakamakon hakan, ita ma Rasha ta saki sojojin Ukarain 95 da ke daure a matsayin fursunonin yaki. Shi ma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a ya fada wa manema labarai cewa a ci gaba da kare mayakan kasar, a yau Laraba sojojin kasar 95 da ke daure hannun Rasha sun iso gida. Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ce dai ta jagoranci musayar fursunoni wace ke nuna alama idan aka samu fahimta duk kasashen biyu da ke yaki da juna, suna iya kawo mayakansu da aka kama a fagen yaki izuwa gida. A watan jiya ne dai shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace sojojin Rasha kimanin 1,348 ke hannun Ukraine, yayinda ita kuwa Rasha take rike da sojojin Ukaraine da aka kama a fagen daga har soja 6,465. Kasashen biyu Rasha da Ukraine duk sun tabbatar cewa ma'aikatun jinkai na kasashen biyu na ci gaba da tattaunawa da juna kan yadda za a samu damar dawo da sojojin da aka kama a fagen yaki izuwa kasashensu.