Museveni ya yi wa 'yan takara barazana
February 19, 2016An dai dauki lokuta da dama a runfunan zaben birnin Kampala na Yuganda da ma yankin Wakiso da ke Arewacin kasar kafin soma zabubbuka, abin da ya janyo fushin jama'a da suka zo domin zaben da ke zargin bangaren shugaban kasar mai barin gado da shirya makarkashiyar tafka magudi a zaben.
Uchenna Emelonye, wakilin babban kwamishinan kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya da ke daya daga cikin masu bin zaben cewa yayi.
" A taikaice dai abin da zamu iya cewa a karon farko dangane da wannan zabe shi ne babban tsaiko da aka samu da kuma kasa isar da kayayyakin zaben ya zuwa wasu runfunan zabe, yayin da wasu 'yan kasar ba su samu damar yin zabe ba a ranar alhamis ba, sannan mun gani da idanunmu yadda aka fuskanci tashe-tashen hankulla a zabukan tsakanin jami'an tsaro da 'yan sanda.
Akalla dai runfunan zabe 36 ne aka bude a wannan Juma'ar tare da ci gaba da zaben kasar ta Yuganda kamar a unguwar Gbaba inda aka fuskanci tashe-tashen hankulla har ma jami'an 'yan sanda sun yi amfani da borkonon tsofuwa wajen tarwatsa mutane. Sai dai a cewar madugun 'yan adawar kasar ta Yuganda Kizza Besigye ya kamata a kawo karshen wannan rishin adalcin da bangaran shugana Moseveni ke nunawa.
" Abun ya isa haka, Idan har Shugaba Museveni baya bukatar a yi wannan zabe, to bai kamata yasa a kira zaben ba, amma kuma idan har aka ce za a yi zabe do dole ne a yi shi sosai kamar yadda ya kamata.
Shi kuwa shugaban mai barin gadi wato Museveni ya yi kashedi yin kashedi yayi ga duk masu tada zaune tsaye ne a kasar.
" Idan har wani ya yi yunkurin tayar da hankali, to zamu saka shi ne cikin na'urar sanyaya ruwa ta friza har sai zucciyar sa ta yi sanyi. A shirye muke ,kuma dukannin sojojin kasar a shirye suke, da jami'an tsaro na 'yan sanda don haka banga wani da zai kawo tashin hankali ba,
Duk dai da cewa 'yan adawar kasar ta Yuganda ba su da matsaya guda wajan tsayar da dan takara guda ba, amma kuma suna da yakinin kaiwa shugaban mai barin gado ga zagaye na biyu a wannan zabe a wannan kasa da ke nesa da teku ta Gabshin Afirka da ba a taba samun canjin mulki ba tun da ta samu mulkin kai a shekara ta 1962.