1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mazauna Saudiyya kadai ne za su yi aikin Hajji

Ramatu Garba Baba
June 23, 2020

Hukumomi a Saudiyya sun fidda sanarwar cewar maniyata aikin Hajji daga kasashen ketare ba za su samu damar yin aikin Hajjin bana ba saboda halin da ake ciki na annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3eBAQ
Saudi-Arabien einsame Pilger in Mekka an der Kaaba
Hoto: AFP

Gwamnatin Saudiyya ta ce mazauna kasar ne kawai za su iya gudanar da aikin hajjin bana, a sanarwar da ta fitar a jiya Litinin , Saudiyyan ta bayar da dalilan daukar matakin ne da zummar hana yaduwar annobar Coronavirus. A bara maniyata kimanin miliyan biyu da rabi daga kasashen duniya sama da dari da hamsin suka gudanar da ibadar mai mahinmanci.

Saudiyya na ci gaba da yakar cutar da tuni ta yi sanadiyar rayuka dubu daya da dari uku yayin da alkaluman wadanda suke kamuwa da cutar ke ci gaba da karuwa, ana da mutum sama da dubu dari da sittin masu Coronavirus a Saudiyya.