1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmai ne za su yi wa APC takara a Najeriya

July 11, 2022

A Najeriya dan takarar shugabancin kasa a jam'iyya mai ci ya bayyana wani Musulmi a matsayin wanda zai taimaka masa a fafatawar da za a yi a zaben kasar na 2023.

https://p.dw.com/p/4Dvsa
Nigeria l APC Ergebnis l Präsidentschaftskandidat
Hoto: Nigeria Prasidential Villa

A Najeriya dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sunan tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Settima a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaben kasar da ke tafe.

Bola Tinubu wanda Bayarbe ne daga yankin Kudu maso yammacin Najeriya, ya sanar da zabin Shettima ne a lokacin gaisuwar Sallah da ya kai wa Shugaba Buhari a garinsa na Daura da ke cikin jihar Katsina.

Wannan zabi na Kashim Shettima dai zai kasance mai cece-kuce a siyasar kasar, ganin cewa dukkaninsu Musulmi ne da wasu ke ganin ba zai kasance adalci ga mabiya wasu addinai ba.

A Najeriya dai tsarin da aka saba da shi, shi ne samun mabiya manyan addinan kasar na Musulunci da na Kirista a takara saboda dorewar hadin kai da fahimtar juna.

Cikin watan jiya ne dai Bola Tinubu mai shekaru 70, ya samu nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC inda yake son ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari da ke kan karaga a halin yanzu.