1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hari ta sama ya halaka mutane 20 a Sudan

Suleiman Babayo ZUD
October 22, 2024

Masu aikin ceton Sudan sun tabbatar da mutuwar mutane 20 a wani hari ta sama yayin da wasu kusan 30 suka jikata a birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar ta Sudan.

https://p.dw.com/p/4m6oA
Yakin Sudan
Yakin SudanHoto: Volunteer Group South Khartoum Emergency Room/Xinhua/IMAGO

Masu aikin agajin ceto na Sudan sun bayyana cewa mutane 20 sun halaka ciki har da yara sakamakon hari hari ta sama a birnin Khartoun fadar gwamnatin kasar, sannan wasu mutanen kusan 30 suka jikata. Haka na zuwa lokacin da rundunar mayar da martanin gaggawa ta halaka wasu mutanen 25 a wani kauye na gabashin kasar.

Kimanin mutane dubu-150 suka halaka sakamakon yakin na Sudan tsakanin dakarun gwamnati da rundunar mayar da martanin gaggawa, tun lokacin da yakin ya barke tsakanin bangarorin biyu a shekarar da ta gabata ta 2023, ana zargin bangarorin biyu na rikicin Sudan da aikata laifukan yaki.