Pakistan mutane 57 sun rasu
January 11, 2015Talla
Wata likita Dr. Seemi Jamali da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce a yanzu haka sun karbi gawarwaki 57 a bangaren bada agajin gaggawa na asibitin koyarwa na Karachi. Ministan sufuri na gundumar Sindh Mir Mumtaz Hussain Jakhrani ya ce hadarin da ya afku tsakanin wata mota kirar Bus da kuma tankar daukar mai ya faru ne yayin da motar kirar Bus kwace tare da yin taho mu gama da tankar daukar man da sanyin safiyar Lahadin nan a wani yanki da ke da nisan kilomita 50 da birnin Karachi na kasar ta Pakistan.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman