1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Mutane biliyan hudu sun yi riga-kafi

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 29, 2021

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa kimanin sama da mutane biliyan hudu ne suka yi allurar riga-kafin corona a duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/3yHE2
Corona Impfstoff Moderna Biontech Pfizer
Chaina na kan gaba a yin allurar riga-kafin corona a duniyaHoto: CHRISTOF STACHE AFP via Getty Images

Da fari dai allurar riga-kafin na tafiyar hawainiya, kafin daga bisani a samu ci gaba. Rahotanni sun nunar da cewa daga cikin alluran riga-kafin biliyan hudu da aka yi a duniya, Chaina ce ke da kaso mafi tsoka, inda aka yi wa mutane biliyan daya da miliyan 600 yayin da aka yi wa mutane miliyan 451 a Indiya a Amirka kuwa mutane miliyan 343 ne suka karbi allurar riga-kafin. A kasashe matalauta ma dai an fara samun riga-kafin, godiya ga shirin rarraba allurar na Covax da kasashe masu karfin tattalin arziki suka samar.