1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane biyu sun rasu a zanga-zangar Masar

November 28, 2014

Wata arangama da ta wakana tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a Masar, tayi sanadiyar rasuwar mutane biyu a unguwar Matariya da ke gabashin birnin Alkahira.

https://p.dw.com/p/1Dwoe
Ägypten Polizei Proteste in Kairo 28.11.2014
Hoto: Reuters/A. Waguih

Akalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon wata arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a kasar Masar, yayin da magoya bayan tsofon shugaban kasar Mohamed Morsi da sojojin kasar suka hembare a watan Yuli na 2013 suka fito domin kalubanantar hukumomin kasar. A kalla dai an kama mutane fiye da 200 daga cikin masu zanga-zangar.

Kungiyar 'yan Salafiyya ce dai ta kasar mai goyon bayan tsofon shugaba Morsi ne ta kira wannan zanga-zangar bayan sallar Juma'a da zimmar neman kifar da gwamnatin shugaba Abdel Fatah Al-sissi wadda tuni aka tura jami'an tsaro suka tarwatsa su. Da ma dai hukumomin na masar sun dauki kwararan matakkai kan wannan lamari inda suka zuba sojoji da 'yan sanda a Alkahira babban birnin kasar, da kuma sauran manyan biranen kasar. A cikin unguwar Matariya ce dai da ke gabashin birnin na Alkahira aka samu arangamar da tayi sanadiyyar mutuwar mutanen biyu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal