Mutane da dama sun halaka a sabuwar girgizar kasar Nepal
May 12, 2015Sama da mutane talatin sun rasu yayin da sama da dubu daya suka sami raunika a sabuwar girgizar kasa mai karfin maki bakwai da digo uku a ma'aunin Richter da ta sake afkawa wani yanki a kasar Nepal a ranar Talatan nan, kamar yadda hukumar kasa da kasa da ke lura da harkokin ‘yan gudun hijira ta IMO ta bayyana.
Paul Dillon jami’in yada labarai na hukumar ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutanen sun rasa rayukansu bayan da wasu gine-gine suka rushe.
Wannan girgiza da ta faru a yankin da ke da duwatsu a tsakiyar ranar Talatan nan ta kuma jawo zaftarewar kasa. Lamarin ya afku kasa da makwanni uku da afkuwar irin wannan bala'i a wannan kasa.
A cewar Laxmi Dhakal jami'i a ma'aikatar harkokin cikin gida a wannan kasa ta Nepal, dukkanin mamatan dai sun rasu ne a lardin Chautara da ke a gabashin birnin Kathamandu da ya fiskanci babban bala’in girgizar kasa a ranar 25 ga watan Afrilu da ya jawo mutuwar mutane sama da 8,000.